Al Qaeda ta karyata labarin mutuwar Belmokhtar
Kungiyar Al-Qaeda a reshen arewacin Afrika ta karyata rahotannin da ke cewa hare haren da Amurka ta kai kasar Libya a makon da ya gabata, sun hallaka tsohon shugabanta Mokhtar Belmokhtar, kamar yadda kungiyar ta sanar.
Wallafawa ranar:
Cikin Sanrwar da ta sanya a shafin Internet a wayewar garin yau Juma’a, kungiyar ta ce mujahid Khaled Abu al-Abbas kamar yadda ake kiransa Belmokhtar, yana nan cikin koshin lafiya.
A ranar Lahadi hukumomin kasar Libya suka fitar da sanarwar mutuwar Belmokhtar, wanda aka dade ana bayar da sanarwa mutuwar shi.
Bangaren mayakan Ansar al Shari’a a Libya da ke da alaka da Al Qaeda sun karyata labarin kisan Belmoktar.
Amurka dai tace ta yi ruwan bama bamai da jiragen sama a inda Belmokhtar ke buya amma ba tare da ikirarin ta kashe kwamandan ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu