Isa ga babban shafi
Algeria

Amurka ta kashen shugaban kungiyar Al-Mourabitoune a Libya

Wani harin da kasar Amruka ta kai a jiya lahadi a kasar Libya, ya yi sanadiyar mutuwar shugaban kungiyar Al-Mourabitoune ta mayakan jahadin kasar Aljeria Mokhtar Belmokhtar, tsohon shugaban kungiyar  Aqmi dake da alhakin kai mummunan harin ta’addanci  kan  mahakar isakar Gaz ta In Amenas, a kasar Algeria da t yi sanadiyar mutuwar mutane da dama akasari baki yan kasashen ketare.  

Hoton Mokhtar Belmokhtar, da aka ciro daga wani hoton video.
Hoton Mokhtar Belmokhtar, da aka ciro daga wani hoton video. AFP PHOTO / HO / ANI
Talla

Belmokhtar da ake yi wa lakabi da suna "Belawar" ("mai Ido daya" da yaren Larabci) a shekarar 2012 ne ya kirkiro kungiyarsa ta wadanda suka sadaukar da jininsu, wace ta kasance wani reshen kungiyar Al-Qaida a yankin kudancin Sahara Aqmi.

A farkon watan mayun da ya gabata , Belmokhtar ya bayyana goyon bayan kungiyar Al-Mourabitoune, ga ta Al-Qaïda tare da musanta cewa yana tare da ta mayakan jihadi Islama Isis.

Majiyar tsaro a kasar Mali ta bayyana shugaban mujahidan Belmokhtar cewa yana cikin kasar Libiya, inda ta nan ne yake ta shirye shiryen yadda zai mamaye yankin Sahara.

An haifi Belmokhtar 1972 a garin Gardaiya dake cikin rairayin saharar kasar Algeria, tun yana matashinsa ya fara yakin jihadi a kasar Afghanistan a 1991, inda anan ne ya rasa idonsa daya.

Bayan dawowarsa gida Algeria a 1993 a farkon yakin basasar kasar, ya shiga kungiyar dakarun Islama GIA wace, aka rusa a 2005, kungiyar da tafi zubar da jinin jama’a a kasar Algeria.

A 1998 ya shiga cikin gungun mayakan Salafiya da ta balle daga GIA, kungiyar da ta shuka ta’addanci da fasakwaurin miyagun kaya a yankin Sahara.

Belmokhtar da mayakansa dai sun shuka ta’addanci na kin karawa a yankin Sahara, ta’addancinsa kuma ya shafi kasashe da dama na yankin Sahel, da suka hada da Mali, Niger, Libiya da kuma kasashen Algeria da Mauritaniya.Ya kuma sha yin garkuwa da yan asalin kasashen Turai, yan karbar, wasun kuma ya yankasu tamkar dabbobi.

A baya dai dakarun Tchadi sun taba bayyana cewa, sun kashe Belmokhtar, a wani gumurzu da aka yi da dakarunsa a kasar Mali, amma daga baya ya sake bayyana a kasar Libiya.

Sai dai duk da cewa, gwamnatin Libiya da kasashen duniya suka amince da ita ta bayyana ya mutuwarsa sakamakon harin na dakarun Amruka, kasar ta Amruka ta ce, ta na ci gaba da binciken kara tabbatar da in shine ta kashe, a harin nata na karshen mako a kasar Libiya.

Amruka ta taba  saka tukuici mai tsoka,  ga duk  wani da ya sanar da ita inda maboyar Belmokhtar  take a yankin Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.