Tsohon shugaban Peru da mai dakin sa zasu gurfana a gaban kotu
A kasar Peru,tsohon Shugaban kasar Ollanta Humala da mai dakin sa Nadine Heredia za su fuskanci kotu kama daga ranar 21 ga watan Fabrairun shekarar bana bisa laifin samun su da hannu a batuttuwan da suka jibanci cin hantsi da rashawa.
Wallafawa ranar:
Ana tuhumar wasu mutane 9 da suka hada da mahaifiyar mai dakin tsohon Shugaban kasar da halasta tareda asasa rashawa da wani kamfanin kasar Brazil yayin yakin neman zaben Shugaban kasar a lokacin..
Tsohon Shugaban kasar Peru Ollanta Humala mai shekaru 59 ya shugabanci kasar ta Peru kama daga shekara ta 2011 zuwa 2016 .
Kotu ta umurci a daure tsohon Shugaban kasar shekaru 20 a kurkuku,yayinda ta bukaci a daure mai dakin sa shekaru 26 kurkuku.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu