Isa ga babban shafi

Amurka ta gargadi gwamnatin kasar Peru dangane da batun kare dan Adam

A yau laraba Amurka ta yi kira da a kawo karshen amfani da karfi’ kan masu zanga-zanga a kasar Peru, ta kuma ce ta goyi bayan kaddamar da wani bincike kan murkushe mutanen da suka yi sanadin mutuwar da dama.

Yan Sandan kasar Peru sun murkushe masu zanga-zanga
Yan Sandan kasar Peru sun murkushe masu zanga-zanga REUTERS - STRINGER
Talla

Har yanzu Amurka ta ce "tana goyon bayan kudurin gwamnatin Peru na gudanar da bincike kan duk mace-mace" da ke da nasaba da zanga-zangar tare da yin kira ga jami'an tsaro da su mutunta doka.

Akalla mutane 40 ne suka mutu yayin da fiye da 600 suka jikkata a zanga-zangar da ta biyo bayan tsige shugaban jam'iyyar gurguzu Pedro Castillo da tsare shi a ranar 7 ga watan Disamba 2022, wanda ake zargi da yunkurin juyin mulki tare da yunkurin rusa majalisar dokokin kasar da ke shirin tsige shi daga mulki.

Babban mai shigar da kara na kasar, Patricia Benavides, ta sanar a yau Laraba cewa, an kaddamar da wani bincike na share fage kan shugabar kasar mai ci Dina Boluarte, dangane da murkushe masu zanga-zangar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.