Isa ga babban shafi

Mutane 17 sun mutu a rikicin siyasar Peru bayan hambarar da shugaba Castillo

Akalla mutane 17 suka mutu yayinda wasu da dama suka jikkata a wata arangama tsakanin jami’an tsaron Peru da masu zanga-zangar da suka nufaci shiga filin jirgin saman kasar a litinin din nan, yayin rikicin da ke ci gaba da tsananta a kasar kusan wata guda. 

Shugaba Pedro Castillo, da Dina ta hambarar sakamakon kama karya kan shirin komawa amfani da dokar Soji.
Shugaba Pedro Castillo, da Dina ta hambarar sakamakon kama karya kan shirin komawa amfani da dokar Soji. AFP - CARLOS MAMANI
Talla

Majiyoyin tsaro a Peru sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa lamarin ya faru ne a kudu maso gabashin birnin Juliaca da ke yankin Puno lokacin da fusatattun masu zanga-zangar suka nufaci yiwa filin jirgin saman birnin tsinke lamarin da ya kai ga arangamar inda nan ta ke mutane 12 suka mutu. 

Bayan fitar da alkaluman farko ne wasu bayanai suka bayyana cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu a arangamar ya karu zuwa 17 bayan samun karin mutum biyar da suka mutu daga cikin mutane fiye da 40 da suka jikkata. 

Kamar mabanbantan gangamin da kasar ke ci gaba da gani cikin fiye da wata guda da ya gabata, suma masu zanga-zangar ta litinin din da ta gabata, na bukatar murabus din Dina Boluarte ne da ke ci gaba da jagorancin kasar bayan hambarar da shugaba Pedro Castillo a ranar 7 ga watan Disamban bara. 

Matakin hambarar da Castillo na zuwa ne bayan yunkurin na rushe Majalisar kasar da nufin fara amfani da dokar Soji dai dai lokacin da ya ke fuskantar zarge-zargen rashawa lamarin da ya haddasa yamutsin makwanni a sassan kasar wadda ta shafe shekaru ta na fama da rikicin siyasa. 

Sai dai fusatattun masu zanga-zangar wadanda ke jin haushin hambarar da Castillo mai sassaucin ra’ayi na ci gaba da nuna fushinsu don ganin dole Boluarte ta yi murabus tare da gudanar da zaben da aka sauyawa wa’adi daga 2026 zuwa 2024. 

Zuwa yanzu alkaluman mutanen da suka mutu daga hambarar da Castillo ya kai mutum 39. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.