Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Boko Haram ta sake hallaka wani babban sojin Najeriya

Wata majiya daga rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa kungiyar Boko Haram ta sake hallaka wani Laftanar Kanal na rundunar, da safiyar Talata.

Sojin Najeriya da ke fagen daga a dajin Sambisa bayan kwace makamai daga hannun mayakan Boko Haram
Sojin Najeriya da ke fagen daga a dajin Sambisa bayan kwace makamai daga hannun mayakan Boko Haram via SK Usman facebook
Talla

Laftanar Kanal B.U. Umar, da ke shugabantar bataliya ta 114 ta rundunar sojin Najeriya tare da wasu sojoji, sun gamu da kwanton Bauna ne daga mayakan Boko Haram yayin da suke kan hanyar zuwa garin Piridang na jihar Adamawa daga garin Bita na jihar Borno.

Kamar yadda wasu jaridu a Najeriya suka rawaito, majiyar sojin ta ce da fari motar da Laftanar Kanal B.U. Umar ta taka nakiya, sai dai babu abin da ya same shi bayan tashinta. Bayan fitowarsa ne daga motar, mayakan na Boko Haram suka bude masa wuta, nan take kuma ya rasa ransa tare da wasu sojoji.

Kawo yanzu dai a garzaya da sojoji 8 zuwa asibiti, yayinda ba’a kai ga tantance yawan wadanda suka rasa rayukansu ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.