Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun kashe 'yan kunar bakin wake

Sojojin Najeriya sun harbe wasu mata uku har lahira bayan sun yi yunkurin kaddamar da harin kunar bakin wake a birnin Maiduguri da ke jihar Borno a yankin arewa maso gabashin kasar.

Mayakan Boko Haram na ci gaba da kai farmaki kan al'mmar Maiduguri da ke Bornon Najeriya
Mayakan Boko Haram na ci gaba da kai farmaki kan al'mmar Maiduguri da ke Bornon Najeriya
Talla

Majiyar jami’an sojin ta ce, matan sun yi damara da bama-bamai ne don kai farmakin a sanyin safiyar yau jumma’a, amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba, in da kuma bama-bamai biyu suka tarwatse bayan kashe maharan a kusa da Mulai.

Tun lokacin da aka saki ‘yan matan Chibok 21 a cikin watan jiya, kungiyar Boko Haram ta zafafa kai hare-haren kunar bakin wake.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno, Damian Chukwu ya dora alhakin yawaitar hare-haren kan shigowar rani, abin da ya bai wa mayakan na Boko Haram damar ratsa hanyoyi don kutsawa cikin birnin Maiduguri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.