Isa ga babban shafi
Najeriya

Za mu ci gaba da kai hare-hare- Shekau

Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya ce za su ci gaba da kai hare hare a Najeriya da makwabtanta a cikin wani sakon bidiyo da aka wallafa a kafar You Tube.

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau HO / BOKO HARAM AFP / AFP
Talla

Sakon bidiyon na dauke ne da muryar Shekau na tsawon awa daya, kuma a cikin bayaninsa ya dauki alhakin hare-haren ta’addanci na kwanakin baya da aka kai a Borno inda aka samu hasarar rayukan sojoji da fararen hula.

Sannan Shekau ya yi barazanar kaddamar da wasu hare-haren a Najeriya da makwabtanta.

Sai dai kuma Shekau ya shafe lokaci mai tsawo yana wa’azi akan da’awar kungiyarsu ta Boko Haram. Sannan a ciki ya ambaci sunan sabon shugaban Amurka Donald Trump yana mai cewa yaki yanzu aka fara.

Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da rundunar sojin na Najeriya ke ci gaba da kokarin kawo karshen kungiyar ta Boko Haram wadda ta kashe mutane fiye da dubu 20 a cikin shekaru bakwai da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.