Isa ga babban shafi

Matatar man Dangote ta sake zaftare farashin man dizel da na man jirgi

Matatar man Dangote a Najeriya ta sanar da sake zaftare farashin man dizel da na man jirgi a kokarin saukaka farashinsa a sassan kasar, matakin da ke zuwa kasa da mako biyu bayan karya farashin farko da matatar attajirin na Afrika ta yi.

Attajirin Afrika Alhaji Aliko Dangote.
Attajirin Afrika Alhaji Aliko Dangote. © Twitter/Dangote Group
Talla

Sanarwar da matatar man ta Dangote ta fitar ta bayyana cewa daga yanzu za ta rika bayar da kowacce litar man dizel guda akan farashin Naira 940 sai kuma litar man jirgi akan farashin Naira 980.

Sanarwar matatar ta Dangote ta bayyana cewa sake zaftare farashin zai shafi masu cinikayyar da ke sayen litar man dizel miliyan 5 zuwa sama yayinda abokanan cinikayyar da za su sayi lita miliyan 1 zuwa sama za su samu man na dizel a farashin Naira 970.

Wannan matakin na zuwa ne a dai dai lokacin da al’ummar Najeriyar ke tsaka da murna kan matakin farko na rage farashin man na dizel zuwa Naira dubu guda da matatar man ta Dangote.

Duk da cewa har yanzu farashin bai sauya a kasuwanni ba, amma akwai fatan matakin ya shafi yanayin hada-hada musamman ta kayaki da akan yi amfani da man na dizel wajen safararsu zuwa sassan kasar.

A jawabinsa game da matakin shugaban sashen hulda da jama’a na matatar ta Dangote Mr Anthony Chiejina ya ce yunkurin wani mataki ne na ganin al’ummar Najeriya sun samu sauki daga matsin rayuwar da suke fama da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.