Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya karbi cikakken bayanin kasafin kudin Najeriya

A yau laraba an gabatar wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da karin bayani a game da kasafin kudin kasar na shekarar bana daga majalisun tarayya kamar dai yadda ya ce ba zai sa hannu a kansa ba sai an yi masa wannan karin bayani.

Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Majalisar dokokin Najeriyar ta zartar da kasafin kudin na kimanin dala biliyan 30 wanda ba a taba kasafi mai yawa irinsa ba.

Tuni dai aka danka wannan kundi a hannun masu bai wa shugaban kasar shawara kan lamurran da suka shafi majalisa Ita Enang da kuma Kawu Sumaila da kundin da ke kunshe da wadannan bayanai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.