Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya ki amince wa da kasafin kudin Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ki rattaba hannu a kan kasafin kudin kasar na shekara ta 2016 bayan majalisar dattawa ta gabatar ma sa da takardun kasafin a makon jiya.

Shugaban Najeriya  Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Wannan al’amari dai zai tsawaita jinkirin aiwatar da kasafin kudin da gwamnatin kasar ke kyautata zaton zai fitar da al’ummar Najeriya daga matsalar tattalin arzikin da ta addabe su.

Wata majiya a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja ta bayyana cewa, Buhari ba zai iya rattaba hannu a kasafin da majalisa ta amince da shi ba saboda bai kunshi bayanai filla-filla ba.

Majiyar ta ce,har yanzu majalisar ba ta aiko wa shugaba Buhari da bayanan kasafin kudin ba.

Majiyar  kara da cewa, Buhari na da burin amince wa da kasafin amma yana fargaban cewa, yin haka ba tare da gamsassun bayanai ba, zai kai ga amince wa da wani bangare da ba za a iya aiwatar da shi ba.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.