Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya fitar da kasafin Kudin shekarar 2016

Gwamnatin Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ta gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2016 da ya kai naira Triliyan 6, kudin da ya zarce kasafin kudin bana da kashi 15.

Shugaban Tarayyar Najeriya,  Muhammadu Buhari
Shugaban Tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Gwamnati ta sanar da kudirinta ne bayan ta kira taron gagawa na majalisar ministocin kasar da aka shafe Sa’o’i uku ana gudanarwa a babban birnin Tarayyar Abuja wanda shugaba Buhari ya jagoranci zaman .

A wata ganawa da manema labarai Jim kadan da kammala taron, Ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Udoma Udoma ya ce, kashi 30 cikin 100 na kasafin kudin zai tafi ne a kan manyan ayyuka.

Al’amarin da ke nuni da cewa Naira tiriliyan 1.8 ake son warewa domin manyan ayyukan a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.