Isa ga babban shafi
Najeriya

Sabbin ministocin Najeriya sun fara aiki

Wasu daga cikin ministoci 36 na Najeriya sun fara aiki bayan shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya rantsar da su a jiya laraba a fadarsa da ke babban birnin Abuja.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ministocinsa.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ministocinsa. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Tuni dai Ministocin suka isa ma’aikatun da za su jagoranta inda suka lashi takobin samar da chanjin da jam’iyyar APC mai mulki ta yi alkawarin kawowa a kasar.

Sabon ministan noma da bunkasa karkara, Audu Ogbeh ya bayyana cewa zai rage kudadden da ake amfani da su da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 32 wajan shigo da abinci a kowace shekara.

Ministan ya ce, akwai kalubale ga ma’aikatar noma kuma za ta sha matsin lamba dangane da tarawa Najeriya kudade, lamarin da zai sa su kara kaimi wajan gudanar da bincike akan harkokin ma’aikatar .

Shima sabon ministan sufuri, Rotimi Amaechi da ake sa ran zai fara aiki gadan-gadan a ranar 17 ga wannan watan, ya bayar da tabbacin cewa zai kammala aikin samar da jiragen kasa da gwamnatin da ta shude ta fara.

A nasa bangaren ministan kwadago, Chris Ngige ya yi alkawarin magance matsalar rashin aikin yi da ke addabar matasa a kasar.

Tsohon gwamnan lagos kuwa, kuma ministan makamashi da ayyuka da samar da gideje, Babatunde Fashola ya bayyana cewa za su gudanar da ayyuka domin magance matsalolin da ake fama da su cikin gaggawa kuma ya ce, yana bukatar cikakkun bayanai game da ayyukan da aka yi a baya da kuma wadanda ba a yi ba, inda a cewarsa, daga nan za su dora.

Fashola ya yi alkawarin tabbatar da wutar lantarki a duk fadin Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.