Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan Najeriya na son a tayar da kamfanin Ajaokuta

Tama da Karafa sun kasance babbar hanyar bunkasar tattalin arzikin kasa musamman ga kasar da masana’antunta suka bunkasa. A yau Amurka da Rasha suna tinkaho ne da arzikin Karafa. Amma Najeriya ta yi watsi da babban Kamfaninta na Ajaokuta wanda aka gina domin samarwa da sarrafa karafa duk da makudan kudaden da kasar ta kashe wajen gina kamfanin.

Kamfanin Sarrafa Karafa na Ajaokuta a Najeriya
Kamfanin Sarrafa Karafa na Ajaokuta a Najeriya RFI Hausa/Awwal
Talla

A yanzu da Najeriya ke neman hanyoyin bunkasa Noma da hako albarkatun kasa don rage dogaro da arzikin fetir, wasu ‘yan Najeriya na ganin farfado da babban kamfanin Ajaokuta na samarwa da sarrafa karafa ne ya kamata Gwamnatin Muhammadu Buhari ta mayar da himma a kai.

 Saboda albarkatun Tama da karafa da Allah ya albarkaci Najeriya ya sa aka gina kamfanin Ajaokuta a Jihar Kogi tsakiyar Najeriya.

Kasar Rasha ce ta gina Kamfanin Ajaokuta a Najeriya
Kasar Rasha ce ta gina Kamfanin Ajaokuta a Najeriya RFI/Awwal

Kasar Rasha ce ta gina kamfanin kuma an kaddamar da shi ne zamanin mulkin Alhaji Shehu Shagari a 1983.

Akwai ma’aikatan kamfanin da dama da suka samu horo a Rasha, amma yanzu yawancinsu sun yi ritaya.

Kamfanin na dauke da dubban ma’aikata wadanda ke ci karkashinsa duk da ba ya cikin koshin lafiya, lamarin da wasu ke ganin gwamnatin Najeriya na matukar hasara saboda babu abin da ta ke samu daga kamfanin.

Cikin Kamfanin Ajaokuta na Najeriya
Cikin Kamfanin Ajaokuta na Najeriya RFI Hausa/Awwal

Mutum dai ba zai fahimci girman kamfanin ba da irin abin da ya kunsa sai idan ya gani da idonsa, musamman irin dukiyar da Najeriya ta batar kuma da aka dakatar da ayyukan kamfanin saboda ba a idar da kammala shi ba.

Shugaban Kamfanin Injiniya Isah Joseph Onebere yace kadan ya rage a idar da ayyukan Ajaokuta.

“An kammala Kamfanin Ajaokuta da kusan kashi 98 a wajajen 1994, shekaru 21 da suka gabata”. A cewar Onebere.

Ana narka Karfe a samar da kayan amfanin Injin a Ajaokuta
Ana narka Karfe a samar da kayan amfanin Injin a Ajaokuta RFI/Awwal

Ya kara da cewa daga cikin sassan kamfanin 43, an kammala 40, kuma yawancinsu an gwada su suna aiki a lokacin.

Mista Onabere ya ce, abin da ya haifar da tarnaki ga ci gaban kamfanin a shekarun da suka gabata shi ne rashin samar da wasu muhimman abubuwa da suka zama wajibi, domin an samar da kamfanin ne ta hanyar fasahar Blast Furnace da ke son aiki ba tsayawa har tsawon shekaru 10 amma abubuwa sun tsaya saboda rashin hanyar jirgin kasa da za a shigo da kayan aiki musamman daga tashar jirgin ruwa a Jihar Rivers zuwa Ajaokuta.

10:06

Shiri na 1: Awwal Janyau ya kai ziyara Kamfanin Ajaokuta

Tun a wajajen 1985 zuwa 87 wasu sassan cibiyoyin kamfanin aka kaddamarsu amma daga baya suka daina aiki, ko da ya ke akwai karafa da ake sarrafawa a yanzu irinsu Rodi da ake amfani a wajen gini da gadoji da kuma wasu karafan da injina ke amfani da su.

Gwamnatoci da dama sun yi kokarin farfado da Kamfanin Ajaokuta amma sun gaza wanda ake ganin ginshiki ne wajen samar da ci gaban kasa da warware matsaloli da dama da yanzu Najeriya ta ke ciki.

Farfado da Kamfanin Ajaokuta na cikin muhimman bukatun Najeriya, musamman yanzu da aka samu sauyin gwamnati da ke da’awar canji.

A lokacin yakin neman zabensa, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawalin farfado da Kamfanin Ajaokuta, amma har zuwa yanzu bayan shafe kwanaki 160 a karagar mulki babu wani yunkuri da gwamnatinsa ta yi akan Kamfanin.

Ko da ya ke a lokacin da ya ke ganawa da Ministocinsa kafin rantsar da su a farkon watan Nuwamba, shugaban ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali ga bunkasa noma da hako ma’adinai don rage dogaro da arzikin fetir.

09:59

Shiri na biyu: Awwal Janyau ya kai ziyara Kamfanin Ajaokuta

Najeriya dai za ta kasance kasa mai dogaro da kanta Idan dai aka farfado da kamfanin, kuma mai fitar da dukkan kayayyakin da suka shafi karafa zuwa kasashen da ke makwabtaka da ita da ketare.

Idan aka farfado da kamfanin Ajokuta, Tattalin arziki Najeriya zai bunkasa da kimiya da Fasaha, sannan ilimi zai karu, za a samu ayyukan yi da kudaden shiga inji Jami’in hulda da Jama’a Kamfanin Muhammed L D Ibrahim.

Sai dai Masana na ganin kamfanin ya kai wani munzalin da yana da wahala a iya farfado da shi cikin lokaci kankani saboda lokacin da aka kwashe ba ya aiki.

Amma Shugaban kamfanin, Isah Onebere ya ce duk da shekarun da aka shafe kamfanin ba ya aiki amma injininsa na cikin koshin lafiya domin ana kula da su.

Hotunan Kamfanin Ajaokuta

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.