Isa ga babban shafi
Najeriya

Obasanjo: An sace kudaden fetir a zamanin Jonathan

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, ya zargi shugaban kasar Goodluck Jonathan da yin sama da fadi da kudaden kasar da yawansu ya kai dala bilyan 25. Obasanjo ya fadi haka ne a garin Abeokuta a lokacin da ya ke ganawa da shugabannin Mata a yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo
Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo Getty Images
Talla

Jaridun Najeriya sun ruwaito tsohon shugaban yana caccakar gwamnatin Goodluck Jonathan kan gazawa a fannoni da dama ga ci gaban kasa.

Obasanjo ya ce kafin ya sauka, gwamantinsa ta bar dala bilyan 25 a cikin asusun ajiyar man fetur, bayan ya biya illahirin basusukan da ake bin kasar, kuma wanda ya gaje shi Marigayi Ummaru Musa ‘Yar’Aduwa ya yi kokarin daga kudaden har suka kai dala bilyan 35.

Obasanjo ya ci gaba da cewa ya bar wasu kudaden dala bilyan 40 a cikin asusun ajiya na waje, wadanda ‘Yar Adua ya yi kokarin dagawa zuwa dala bilyan 60 kafin rasuwarsa. Amma yace abin da ya rage a kudade a yau bai wuce dala bilyan 30 ba a zamanin Goodluck Jonathan.

Tsohon shugaban yace ba wai yana fada ban e da Jonathan illa ya damu da halin da Najeriya ta shiga.

A cikin Kalamansa, Obasanjo yace yanzu dam ace ga ‘yan Najeriya su zabi shugaba na nagari a zaben watan Fabrairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.