Ba zan sanya hannu a kasafin Najeriya ba- Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ba zai sanya hannu a kasafin kudin kasar na shekarar 2016 ba da majalisar dattawan kasar ta mika ma sa bayan ta amince da shi.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Buhari ya fadi haka ne a birnin Washington na Amurka inda ya ce, zai duba kasafin filla-filla kafin ya sanya ma sa hannu.
A lokacin da ya ke ganawa da sakataren harkokin wajen Amurka Johan Kerry a jiya Alhamis, Buhari ya ce, ya na bukatar sake nazarin kasafin domin tabbatar da cewa ba a sauya bayanan da ke cikinsa ba.
Buhari ya kara da cewa, wasu jami’an gwamnati sun sauya wasu abubuwa da fadar shugaban kasa ta saka a cikin kasafin, inda suka sanya abinda suke bukata.
Shugaban ya jaddada cewa, zai duba kasafin da aka ware wa kowacce ma’aikata a Najeriya don tabbatar da cewa ya yi dai dai da abinda fadarsa ta gabatar wa majalisa tun a farko.
A bangare guda, shugaba Buhari ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da yaki da matsalar cin hanci da rashwa yayin da John Kerry ya ce, Amurka za ta taimaka wa Najeriya wajen mayar ma ta da kudaden da aka sace kuma aka boye su a bankunan Amurka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu