Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugaban Najeriya zai halarci taron MDD a Amurka

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi kasar Amurka a ranar alhamis inda ake sa-ran zai yi jawabi a gaban zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York a ranar litinin.

Babban magakatardar MDD Ban Ki-Moon (dama) yana musabaha da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Abuja.
Babban magakatardar MDD Ban Ki-Moon (dama) yana musabaha da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Abuja. AFP Photo/Sunday Aghaeze via yahoo
Talla

Fadar shugaban Najeriyan ta ce a lokacin ziyarar Buhari zai gana da babban magatakarda na MDD Ban Ki-Moon, da shugaban Amurka Barack Obama da na Faransa Francois Hollande.

Femi Adeshina mai Magana da yawun shugaban Najeriya, ya Muhammadu Buhari zai tattauna da Firaminsitan Birtaniya David Cameron, da shugaba Xi Jinping na china, da shugaba Vladimir Putin na Russia da Firaministan India Narendra Modi da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

Adeshina ya ce bayan taron, shugaba Buhari zai gana da tsohon shugaban Amurka Bill Clinton da attajiri Bill Gates, da matar sa Milinda Gates da tsohon Firaministan Birtaniya Gordon Brown sannan ya kammala ziyararsa a ranar 29 ga wata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.