Isa ga babban shafi
Najeriya-Amurka

Buhari yana ziyara a Amurka

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fara ziyara a kasar Amurka, inda ake sa rai zai gana da shugaban Amurkan Barak Obama, kan batutuwan da suka shafi huldar kasashen biyu da kuma yadda za a yi yaki da ta’addanci.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Amurka
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Amurka saharareporters
Talla

Sanarwar da fadar shugaban Najeriya ta fitar, ta bayyana cewa shugabannin biyu zasu mayar da hankali kan sha’anin bunkasa tattalin arziki da tsaro.

Shugaba Buhari zai gana da shugaba Obama a fadar gwamnatin Amurka ta White House, inda ake sa ran za su tattauna matakan da za a bi domin kawo karshen ayyukan Boko Haram da kuma matakan ceto ‘Yan matan garin Chibok da mayakan suka sace.

03:08

Malam Shehu Garba mai magana da yawun Shugaba Buhari

Nasiruddeen Mohammed

Malam Shehu Garba da ke magana da yawun Buhari ya ce ziyarar wata dama ce ta kokarin farfado da huldar Najeriya da Amurka, musamman yadda Shugaba Obama ke kaucewa Najeriya a ziyarar da ya kawo a Afrika.

Buhari ya tafi Amurka ne tare da rakiyar Gwamnonin Jihohin Edo da Nasarawa da Imo da Borno tare da Tunde Bakare da tsohon gwamnan Jihar Rivers Rotimi Ameachi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.