Isa ga babban shafi
Najeriya

Muhimman batutuwan da Buhari zai tattauna da Obama

Fadar Shugaban Najeriya ta fitar da jadawalian ayyukan da shugaban kasar Muhammadu Buhari zai yi a ziyarar da zai kai ta kwana hudu a kasar Amurka a karshen wannan mako.

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Sanarwar da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya sanyawa hannu ta bayyana cewar shugaba Muhamamdu Buhari zai mika zuwa Amurka a Ranar Lahadi sannan zai gana da shugaba Barack Obama ranar litinin inda za su tattauna kan matsalar tsaro da yaki da ta’adanci.

Shugaba Buhari kuma zai gana da Babban Hafsan tsaron Amurka, Janar Martin Dempsey da mataimakin Sakataren tsaron kasar Robert Work kan hadin kai tsakanin ayyukan soji.

Shugaban kasar na Najeriya zai kuma gana da mataimakin shugaban Amurka Joe Biden da Sakataren Shari’ar kasar da na kasuwanci da kuma ciniki.

A karshe shugaba Buhari zai gana da kwamitin harkokin waje na Majalisar Amurka da kwamitin Yan Majalisu bakaken fata da ke Majalisar, sannan zai yi jawabi ga Majalisar ‘yan kasuwa ta kasar da Majalisar Yan Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.