Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane sama da 40 sun mutu a hare haren Jos

Mutane sama da 40 suka rasa rayukansu a jerin hare haren bama-bamai guda biyu da aka kai a garin Jos babban birnin Jihar Filato a arewacin Najeriya. Sannan Mutane kusan 50 suka jikkata a hare haren da aka kai a cikin daren Lahadi.

Mutane kusan 40 aka kashe a hare haren garin Jos a Najeriya
Mutane kusan 40 aka kashe a hare haren garin Jos a Najeriya france 24
Talla

Wasu ‘Yan bindiga ne suka kai hari a wajen tafsirin shugaban malaman kungiyar Izala Sheikh Sani Yahya Jingir na Azumin watan Ramadana, daga bisani suka tayar da bam a kusa da Masallacin na Unguwar ‘Yantaya.

Malam Jingir ya ce yana cikin tafsiri ‘Yan bindiga suka fara harbe harbe tare da tayar da bom a kusa da motarsa.

Hukumar agajin gaggawa ta NEMA ta ce mutane da dama suka jikkata a harin, wanda ya zo jim kadan bayan wani bam ya tashi a wajen cin abinci da ke kusa da tashar Bauchi road a garin na Jos a cikin dare.

Wasu mazauna garin Jos sun ce da misalin karfe 9 na dare bom ya tashi a tashar Bauchi road.

Ana zargin mayakan Boko Haram ne suka kai harin wadanda suka dade suna addabar arewacin Najeriya da hare haren bama bamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.