Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojoji sun fatattaki Boko Haram da ke kokarin kutsawa cikin Maiduguri

A cikin daren juma’ar da ta gabata, wasu da ake zaton cewa magoya bayan kungiyar Boko haram ne sun share tsawon sa’o’i akalla biyu suna fafatawa da dakarun gwamnatin Najeriya a wani wuri da ke wajen birnin Maiduguri na jihar Borno.

Sojojin Najeriya a garin Maiduguri, ranar 30 yulin 2009.
Sojojin Najeriya a garin Maiduguri, ranar 30 yulin 2009. (Photo : AFP)
Talla

Shaidu sun ce wasu ‘yan bindiga ne suka yi kokarin mamaye kauyen Zabarmari mai tazarar kilomita 10 daga Maiduguri, to sai dai sojojin na gwmanatin sun yi nasarar fatatakarsu.

A cikin kwanaki biyu da suka gabata, hare-haren da ake dangantawa da kungiyar ta Boko Haram sun yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 200 a sassa daban daban na jihar ta Borno.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.