Isa ga babban shafi
Chadi

Chadi ta sanar da kama Shugabannin Boko Haram

Makwanni biyu bayan faruwar munanan hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 36 a birnin Ndjamena na kasar Chadi, hukumomi a kasar sun sanar da gano dimbin makamai tare da kama da dama daga cikin shugabannin kungiyar Boko Haram da ake zargi da hannu wajen kai wadannan hare-hare.

Daya daga cikin barnar da harin Boko Haram ya yi a Chadi
Daya daga cikin barnar da harin Boko Haram ya yi a Chadi REUTERS/Moumine Ngarmbassa
Talla

Sanarwar da hukumomin kasar ta Chadi suka fitar na cewa bayan cafke wasu da ake zargin cewa magoya bayan kungiyar ta Boko Haram ne a birnin na Ndjamena, an tatsi muhimman bayanai daga wadanda aka cafken, lamarin da ya bai wa jami’an tsaron damar kaddamar da samema a wasu gidaje da ke birnin.

Sanarwar ta ce a lokacin wannan samame, an gano makamai da dama, da suka hada da rokoki manyan da kanana, bindigogi kirar Kalachnikov sannan kuma da albarusai, wata alama da ke tabbatar da cewa mayakan kungiyar sun shirya kai wasu hare-hare da dama a cikin kasar ta Chadi.

Hakazalika hukumomin sun sanar da gano wasu muhimman takardu dauke da sunayen mutane, da suka hada da wani mai suna ‘Moussa Oumar’’ wanda aka haifa a garin Fotokol na kasar Kamaru, amma kuma zuwansu  Chadi, ya sami lasisin tukin mota mai dauke da suna zuwa Moussa Marou.

A yanzu dai babban abinda jami’an tsaron kasar ke kokarin ganowa shi ne inda aka fito da wadannan makamai da kuma yiyuwar akwai wasu dimbin makamai da ke boye a sassan kasar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.