Isa ga babban shafi
Faransa-Chadi-Boko Haram

Hollande ya ce Boko Haram ce ta kai harin Chadi

Shugaban Kasar Faransa Francois Hollande ya ce babu tantama kungiyar Boko Haram da ke Najeriya ce ta kai mummunan harin da ya hallaka mutane 24 da jikata wasu 100 a kasar Chadi.

Shugaban Kasar Faransa, Francois Hollande
Shugaban Kasar Faransa, Francois Hollande (©Reuters)
Talla

Yayin da ya ke jawabi bayan ganawa da shugaban kasar Algeria, Abdelaziz Bouteflika, shugaba Hollande ya yi alkawarin hukunta wadanda suka kai harin da kuma alkawarin taimakawa hukumomin Chadi.

Rahotanin dai na cewa a yau Talata, an iske Jami’an tsaro da dama, da suka hada da Sojoji da ‘Yan sanda na ta kai kawo a kasar domin samar da tsaro.

Har yanzu dai babu wata kungiya da ta dau alhakin kai wa nan harin, irin sa mafi muni karon farko a N’djamena.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.