Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande: Faransa zata kare mabiya Addinai

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya ce Musulmi ne suka fi shan wahala a hare haren da ake kai wa na ta’addnci, yayin da cikin mutane 17 da aka kashe a harin Paris, biyar daga cikinsu musulmai ne. Hollande ya ce Faransa zata kare dukkanin mabiya addinai a kasar mai yawan musulmi a Turai.

Shugaba Francois Hollande na Faransa
Shugaba Francois Hollande na Faransa REUTERS/Charles Platiau
Talla

A lokacin da ya ke jawabi a wata cibiyar yada al’adun larabawa ta duniya a birnin Paris, Hollande ya ce Musulmi ne suka fi shan wahala a hare hare ta’addanci da ake kai wa, yana mai jaddada cewa Faransawa za su hada kai domin yaki da ta’addanci a kasar.

Faransa ce dai ke da yawan musulmi a kasashen Turai, kuma Hollande yace musulmi suna da ‘yanci kamar sauran mutane a Faransa, don haka ya zama wajibi a kare ‘yancinsu.

A yau Alhamis ne  aka yi Jana’izar mutanen da aka kashe a hare haren martani da aka kai wa Mujallar Charlie Hebdo bayan ta yi wani zanen mutum da ya ci zarafin Musulmi.

Mujallar kuma ta sake wallafa zanen da ke nuni da Manzo SAW, wanda ya fusata musulmi, amma Hollande ya ce Mujallar zata ci gaba da ayyukanta.

Wannan al’amarin da ya faru ya janyo muhawara a Faransa game da shata iyaka ga ‘Yancin fadin albarkacin baki da wasu ke ganin ana fakewa domin cin mutuncin musulmi sabanin dokar da aka kafa ta haramta kyamatar Yahudawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.