Isa ga babban shafi
Chadi

Chadi ta yi wa Boko Haram luguden wuta da jiragen sama

Jiragen yakin Kasar Chadi sun yi wa Boko Haram luguden wuta a wasu wurare 6 da mayakan ke buya a Najeriya. Sojin kasar sun ce wannan na a matsayin martani ga hare haren bama bamai da mayakan suka kai a N’Djemena fadar gwamnatin kasar.

Rundunar Sojin Chadi a N'Djamena
Rundunar Sojin Chadi a N'Djamena Thomas SAMSON/Gamma-Rapho via Getty Images
Talla

Wani Mazaunin yankin tafkin Chadin, da bai so a bayyana sunan shi ba, ya tabbatar wa RFI Hausa da aukuwar harin.

Gwamnatin Chadi ta kuma bayyana haramta wa Mata sanya Hijabi da ke rufe fuska saboda dalilai na tsaro bayan harin da Boko Haram ta kai inda mutane 33 suka mutu, sama da 100 suka samu rauni.

Sai dai al’ummar kasar na ci gaba da bayyana adawa da matakin haramtawa Mata sanya hijabi saboda ba Mata ba ne suka kai hare haren da aka kai a kasar.

A ranar Litinin ne dai aka ka iwa Babban Ofishin ‘Yan sanda hari a N’Djamena, wanda shi ne hari na farko da aka kai a birnin.

Zuwa yanzu babu kungiyar da ta yi ikirarin kai harin amma ana zargin Mayakan Boko Haram ne da ke addabar kasashen da ke makwabtaka da Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.