Isa ga babban shafi
Nigeria

Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kai hare hare a Najeriya

Kungiyar Jama’atu Ahlul Sunnah Lidda’awati wal Jihad, da ake kira Boko Haram a Najeriya tace ita ta kai hare haren a wasu sassan jihar Borno da suka lakume rayukan mutane da dama, da kuma hallaka fitatchen malamin nan Sheikh Auwal Albani a garin Zariya, duka a arewacin kasar.Kungiyar ta bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ta fitar, wanda shugaban ta Abubakar Shekau yayi bayani, inda yake cewa su suka kashe sanannen malamin addinin Islaman nan, Sheikh Muhammad Awwal Adam Albani.An dai kashe malamin ne a Zaria tare da matar sa da dan su daya.Kungiyar ta kuma yi ikrarin daukar alhakin hare haren da aka kai Jihar Barno, wanda ya kaiga rasa rayukan mutane da dama.Shugaban kungiyar Abubakar Shekau yace zasu kaddamar da sabbin hare hare kan wasu Yan siyasar Najeriya dake goyan bayan tsari irin na demokradiya.Gwamnatin Najeriya dai tace tana samun nasarar yaki da take da ‘ya ‘yan kungiyar, sabanin ikrarin da ake cewa kungiyar ke nasara. 

Wasu 'yan bindiga a Nigeria
Wasu 'yan bindiga a Nigeria Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.