Isa ga babban shafi
Nigeria

Jami'an tsaro a Nijeriya sun sako wasu iyalan 'yan kungiyar Boko Haram

Soji a tarayyar Najeriya sun bayyana sakin akalla Mata 58 da kananan Yara, iyalan ‘yan kungiyar jama’atu Ahlus sunna, Lil Da’awati Wal Jihad, da aka fi sani da Boko haram.Wannan dai kamar yanda Sojin suka bayyana, wani bangare ne na kyautatawa mutanen domin samar da zaman lafiya a yankin Arewa maso gabashin kasar.Yaro mafi karancin shekaru da aka fitar ya shaidawa Soji cewar shekarar sa 9.Akalla dai an sake Mata 20 a jihar Borno, sai wasu 38 a makwabciyar ta Yobe.Mai Magana da Yawun Dakarun Sojin kasar da ke aikin samar da tsaro a yankin, Lieutenant Eli Lazarus ya bayyana fatan sakin Muatanen zai taimaka a cimma manufar da suka sanya a gaba.Sai dai masu lura da al’amurra na ganin cewar matan ba murnanr sakin su zasu yi ba tunda basu san inda mazajen nasu suke ba a halin yanzu. An shafe fiye da shekaru 2 ana fito na fito, tsakanin jami’an tsaron tarayyar Najeriyar da ‘yan kungiyar ta Boko Haram. 

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau
Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau AFP PHOTO / YOUTUBE
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.