Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun yi watsi da ikirarin Boko Haram

Rundunar Sojan Najeriya ta yi watsi da ikirarin da shugaban Kungiyar Boko Haram ya yi cewa sun fatattaki sojin kasar daga jihohin Yobe da Borno da Adamawa inda aka kafa dokar ta baci domin farautar ‘ya’yan kungiyar.

Dakarun Sojin Najeriya
Dakarun Sojin Najeriya REUTERS/Stringer
Talla

A wani Hoton Bidiyo da kamfanin Dillacin Labaran Faransa na AFP ya samu, shugaban Kungiyar Boko Haram Imam shekau yace sun fatattaki sojin Najeriya a gumurzun da suke da juna.

“Wane irin nasara suke samu da har suke tserewa daga wuraren da ake fafatawa” a cewar kakakin sojin Najeriya Birgediya Janar Chris Olukolade a lokacin da ya ke mayar da martani ga ikirarin na Boko Haram.

"Me yasa suka tsere kuma suka warwatsu idan har suna samun nasara”, inji Olukolade.

Sai dai kuma kakakin na Soja ya ki bayyana adadin mayakan kungiyar da suka kashe ko kuma wadanda suka cafke tun da shugaba Goodluck ya kafa dokar ta baci a jahohin Yobe da Borno da kuma Adamawa.

A cikin sakon bidiyon, Imam Shekau ya yi kira ga mayaka daga kasashen waje su kawo gudunmuwa a yakin da suke yi a Najeriya.

Tuni dai rundunar Sojin Najeriya ta yi ikirarin tarwatsa sansanin mayakan na Boko Haram a Maiduguri.

Dubban mutane ne kuma suka tsere daga yankunan arewa maso gabaci da ke cikin dokar ta baci zuwa makwabtan Jahohi, wasu kuma suka tsallaka zuwa makwabtan kasashe, Nijar da Kamaru wadanda ke kan iyaka da Jahohin Borno da Yobe da Adamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.