Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta yi ikrarin samun nasara a kan dakarun Najeriya

Kungiyar Boko Haram ta fito da wani sabon Bidiyo da ke nuna Shugabanta, Imam Abubakar Shekau yana bayani akan irin nasarar da suka samu a kan dakarun Najeriya da ke ci gaba da farautarsu bayan kafa dokar ta baci a jihohi uku dake Arewa maso gabashin Najeriya.

Shugaban Kungiyar Boko Haram a Najeriya Iman Abubakar Shekau a sakonsa ga shugaba Jonathan.
Shugaban Kungiyar Boko Haram a Najeriya Iman Abubakar Shekau a sakonsa ga shugaba Jonathan. REUTERS/IntelCenter/Handout
Talla

Wannan bayanin bidiyo shine magana ta farko da ta fito daga bakin shugaban kungiyar tun bayan kafa dokar ta baci a Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Shugaban har ila yau a bayanin da ya yi, ya yi kira ga kungiyoyon Islama na kasashen waje da su shiga fadan.

Hotan bidiyon wanda ya nuna Imam Shekau a zaune sanye da rigar soji da rawani da kuma bindiga kirar AK 47 a gefen shi, bai bayyana ko daga ina ya yi magana.

Wannan ikrarin kungiyar ya yi karo da sanarwar da dakarun Najeriya ke fitar a ‘yan kawanakin nan dake cewa suna samun nasara a farautar da suke yin a ‘yan kungiyar.

Dakarun na Najeriya sun bayyana cewa sun yi nasarar fatattakar ‘yan kungiya tare da mallake wasu matsugunansu inda suka kuma kama wasu daga cikinsu.

Kalubalen da ake fuskanta na rashin wayar sadarwa da datse hanyoyin isa wasu yankunan da ake farautar ‘yan kungiyar na kawo cikas wajen tabbatar da ikrarin da bangarorin biyu ke yi.

Kungiyr dai ta bayyana cewa dakarun na Najeriya sun zubar da makamansu sun arce a lokacin da ake fafatawa, inda aka karbe da yawa daga cikin motocinsu da makamai.

A daya bangaren, hukumomin kasar Ghana wacce ke makwabtaka da kasar ta Najeriya sun ba da shawara da Najeriyar ta dauki matakan magance matsalar tsaronta.

Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyara a kasar Faransa a jiya.

“Matsalar tana damun mu a Ghana, domin Najeriya babbar kasar ce a yammacin Afrika, ta fannoni da dama, idan akwai matsala a Najeria abu ne mara kyau ga sauran kasashen Afrika.” Inji Mahama.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.