Isa ga babban shafi
Najeriya

An sassauta dokar hana fita da aka kafa a birnin Maiduguri.

Hukumomin tsaro a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya, sun sanar da sassauta dokar hana fita da suka kafa a wasu unguwanni 12 da ke birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar da ke fama da matsaloli na rashin tsaro.

Sojojin Najeria a kan wani titi na Maiduguri
Sojojin Najeria a kan wani titi na Maiduguri REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Wata sanarwa da rundunar hadin gwiwa mai gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a jihar ta fitar, ta ce a yanzu dokar tana aiki ne daga karshe 7 na safe zuwa karfe biyar 5 na marece, kuma sassauta dokar zai bai wa jama’a damar fita domin yin cefane da kuma biyan wasu bukatunsu.

Jihar Borno dai na daga cikin jihohin kasar uku da aka kafa dokar ta baci a cikinsu, sauran jihohin kuwa su ne Yobe da kuma Adamawa, wadanda a cewar hukumomi suna fuskantar matsalaloli sakamakon ayyukan kungiyar Boko Haram a cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.