Isa ga babban shafi
Najeriya

Dakarun Najeriya sun yi ikrarin cafke ‘Yan kungiyar Boko Haram 120

A Najeriya, dakarun kasar sun ce sun yi nasarar cafke ‘Yan kungiyar Jama’atu Ahlil Sunnah lid Da’awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram su kimanin 120 bayan sun kai masu farmaki a lokacin da suke yi ‘yan kungiyar ke jana’izar daya daga cikinsu.

Dakarun Najeriya, Maiduguri
Dakarun Najeriya, Maiduguri REUTERS/Tim Cocks
Talla

Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya na NAN ya ruwaito kakakin Sojin kasar Brigadier General Chris Olukolade, yana cewa Kwamandan ya mutu ne bayan sun yi musayar wuta da dakarun Soji a Maiduguri.

Kuma yanzu haka dakarun na Najeriya sun yi nasarar kwato yankunan da suka fada ikon kungiyar Boko haram wato Marte, Hausari, Krenoa, Wulgo da kuma ChikunNgulalo da ke Jahar Borno bayan sun tarwatsa sansanin Mayakan na Boko Haram.

Wasu bayanai na cewa Najeriya ta rufe kan iyakokinta da Nijar da chadi da Kamaru da ke kusa da yankunan Arewa maso gabaci domin dakile kwararar mayaka a kasashen
Wannan dai na zuwa ne bayan Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta baci a Jahohin Borno da Yobe da Adamawa domin yaki ta’adanci a yankunan

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.