Isa ga babban shafi
Najeriya

An kashe 'yan Boko Haram 56 a arewacin Nigeria

Rundunar sojin tarayyar Najeriya ta ce dakarunta sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram akalla 56 a hare-hare na baya-bayan nan da ta kai akan maboyar magoya bayan kungiyar a arewa maso gabashin kasar.Kakakin babbar rundunar sojan kasar ta 7 da ke kula da wannan shiyya Keftin Aliyu Danja, shi ne ya bayyana hakan a wata sanar da ya fitar, yana mai cewa dakarunsu sun kaddamar da wani farmaki ne akan mayakan kungiyar daga ranar 28 ga wannan wata a wasu wurare da ke cikin yankin Bama na jihar Borno.A wani bangaren kuma, mutane 12 ne suka mutu sakamakon wani harin da ‘yan bindiga suka kai wa masu bukin aure a karshen makon day a gabata a jihar ta Borno.Kwamishinan ‘yan Sanda Lawan Tanko y ace mutane 2, a kan babur ne suka bude wuta a kauyen Tashan Alade, da akasarin mazaunan shi kiristoci ne, mai nisan Kilimita 230 daga birnin Maiduguri.Kwamishinan ya ara da cewa maharan, da ake zargi ‘yan kungiyar Boko Haram ne, sun tsere, kafin a sami dauki daga jami’an tsaro, sakamakon rashin ingantattun hanyoyin sadarwan da za a tuntubi jami’an tsaro.Wani da lamarin ya faru a kan idon shi yace maharan sun yi shigar bultu, suka saje da bakin da suka je don taya ma’auratan murna. 

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau
Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau AFP/File
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.