Isa ga babban shafi
Najeriya

Rikicin Boko Haram na iya shafar wasu kasashen Afrika, inji Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yace rikicin kungiyar Boko Haram, na iya zama babbar barazana ga sauran yankunan kasasashen Nahiyar Afrika idan har ba a yi kokarin magance matsalar ba.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a zauren taron tattalin arzikin Duniya a birnin Davos
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a zauren taron tattalin arzikin Duniya a birnin Davos REUTERS/Pascal Lauener
Talla

Shugaba Jonathan ya fadi haka ne a lokacin da ya ke zantawa da kafar yada labaran Talibijin ta CNN, ta kasar Amurka, inda kuma ya musanta zargin fatara da talauci ne suka haifar da rikicin Boko Haram a Najeriya tare da karyata zargin da ake wa Dakarun kasar na zarafin al’umma da sunan yaki da Boko Haram.

A kwanan baya kunkiyoyin kare hakkin Bil’adama na Duniya sun zargi Jami’an tsaron Najeriya da keta hakkin fararen hula da sunan yaki da kungiyar Boko Haram.

Najeriya ita ce ta jagoranci Tagawar ECOWAS domin kakkabe Mayakan Mali, kuma Shugaba Jonathan ya yi alkawalin bayar da goyon baya wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar.

A cikin jawabin Jonathan, Shugaban yace akwai alaka tsakanin Kungiyar Boko Haram da Mambobin kungiyar al Qaeda a reshen Arewaicn Afrika da ke yaki a Mali.

“Hakan ya sa Najeriya a shirye ta ke ta hada karfi da sauran kasashe don kawo zaman lafiya a kasar Mali” inji Jonathan.

Gwamnatin Najeriya ta yi alkawalin aikawa da dakaru 900 zuwa Mali.

Shugaban kuma ya karyata rashin samun Shugabanci ne na gari da Cin hanci da rashawa suka haifar da rikicin Boko Haram bayan tambayarsa ko hakan ne musabbin rikicin.

Jonathan yace Kungiyar Boko Haram kungiya ce ta ‘Yan ta’adda.

Yawancin ‘Yan Najeriya dai suna rayuwa ne kasa da Dalar Amurka duk da Arzikin Man Fetir da Allah ya azurta kasar da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.