Farashin mai ya tashi a kasuwar duniya
Farashin Danyan man fetur a kasuwanin duniya ya tashi daga Dala 99 da Centi 66, zuwa Dala 111, da Centi 14, saboda matsalolin da ake samu a Najeriya da Iran cikin manyan kasashe masu samar da mai a kasuwar duniya bayan karfafa Takunkumi da kasashen Turai suka kakabawa Iran da yajin aikin da aka kwashe mako guda ana gudanarwa a Najeriya.
Wallafawa ranar:
Masana tattalin arzikin sun bayyana cewar, yajin aikin da aka kwashe tsawon mako guda ana gudanarwa, da takunkumin da kasashen Turai suka kakabawa kasar Iran na iya daga farashin fiye da yadda yake yanzu.
Kasar Iran da Najeriya suna cikin manyan kasashen da ke fitar da mai a kasuwar duniya.
Takunkumin da Amurka da kasashen yammaci suka karfafa wa Iran yasa wasu kasashen yankin Asiya da Turai neman wata hanyar samun mai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu