Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugaban Najeriya ya dawo da Farashin Mai N97 tare da girke Sojoji a Lagos

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya rage farashin mai daga N141 zuwa N97, kusan kashi 30 domin kawo karshen zanga-zanga da yajin aikin da ma’aikata ke ci gaba da gudanarwa a cikin kasar, yanzu haka kuma Sojoji sun mamaye babban dandalin da ake gudanar da zanga-zanga a Jahar Legas.

Masu Zanga-zangar adawa da janye Tallafin Man fetur a jahar Lagos Tarayyar Najeriya.
Masu Zanga-zangar adawa da janye Tallafin Man fetur a jahar Lagos Tarayyar Najeriya. Save Nigerian group
Talla

Shugaban ya gabatar da jawabi ne a kafar Telebijin din kasar da safiyar yau Litinin, bayan kwashe tsawon mako daya ana gudanar da zanga-zanga a sassan yankunan kasar.

A jawabin shugaban yace, wasu sun karbe zanga-zangar domin kokararin tayar da hanakli a cikin kasar.

02:32

Abdulwahid Umar, Shugaban kungiyar Kwadago

Kungiyar kwadago da kungiyoyin fararen hula sun ce zasu ci gaba da gudanar da yajin aiki, kodayake sun yi kiran kawo karshen zanga-zanga saboda Fargabar matsalar tsaro da shugaba jonathan ya yi gargadinsu akai.

A Jawabin Shugaban, yace gwamnatinsa zata ci gaba da shirinta na janye Tallafin mai.

Sai dai yace bisa halin da ‘yan kasar suka shiga bayan tattaunawa da gwamnoni da shugabannin Majalisa, gwamnati ta dawo da farashin mai zuwa N97.

03:56

Alh Aliyu Abubakar

Bashir Ibrahim Idris

A ranar 1 ga watan Janairu ne Gwamnatin Jonathan ta janye Tallafin Mai matakin da ya haifar da linka farashin mai daga N65 zuwa N141, al’amarin da ya fusata ‘yan Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.