Isa ga babban shafi
Iran-Najeriya

Farashin Mai ya tashi a duniya bisa rikicin Iran da Najeriya

Farashin danyen mai ya tashi a kasuwar duniya sanadiyar rikicin kasashen yammaci da kasar Iran da kuma zanga-zangar adawa da janye Tallafin mai da ke ci gaba da kadawa a Tarayyar Najeriya. Takunkumin da Amurka da kasashen yammaci suka karfafa wa Iran yasa wasu kasashen yankin Asiya da turai neman wata hanyar samun mai.

Masu Zanga-zangar adawa da janye Tallafin Man fetur a jahar Lagos Tarayyar Najeriya.
Masu Zanga-zangar adawa da janye Tallafin Man fetur a jahar Lagos Tarayyar Najeriya. Save Nigerian group
Talla

Tuni dai kasar Iran ta dauki matakin toshe mashingin ruwan Hormuz domin kawo cikas ga kasuwar mai bayan takunkumin da kasashen Yammaci suka kakuba mata akan zargin kasar da karfafa shirinta na Nukiliya.

A Najeriya kuma dubun dubatar ‘yan kasar ne suka fito a sassan yankunan kasar domin nuna rashin amincewarsu da matakin gwamnati na janye tallafin mai, hanyar da ‘yan kasar suke ganin ita ce suke more arzikin mai da Allah ya albarkaci kasar da shi.

00:34

Labaran Maku,Ministan yada labaran Najeriya

Kasar Iran da Najeriya suna cikin manyan kasashen da ke fitar da mai a kasuwar duniya.

A yau Alhamis ne aka shiga kwanaki hudu na yajin aikin ma'aikata da Zanga-zangar adawa da janye Tallafin mai a Najeriya sai dai har yanzu gwamnatin kasar ta sake jaddada cewar, ba zata waiwaya baya ba game da mayar da tallafin bayan zaman Majalisar Ministocin kasar.

Sai dai kuma Majalisar wakilai da majalisar dattawa sun hada hannu domin sasantawa da bangaren zartaswar kasar domin daukar matakin kawo karshen yajin aikin da aka kwashe kwanaki hudu ana gudanarwa.

02:45

Wakilinmu daga Ghana, Rilwan Abbas

Wakilinmu daga kasar Ghana yace 'yan Najeriya mazauna kasar sun gudanar da zanga-zangar adawa da janye tallafin tare da mika sako ga jekadan kasar zuwa ga shugaba Goodluck Jonathan don mayar da tallafin da al'ummar Najeriya ke amfana da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.