Isa ga babban shafi
Najeriya

Sakon Boko Haram ga Shugaban Najeriya.

Shugaban Jama’atu ahlis Sunna lidda’awati wal Jihad da aka lakawa sunan Boko Haram yace shugaba Goodluck jonathan baya da ikon hana su daukar fansar kisan ‘yan uwansu da aka yi, a wani sako da kungiyar ta yada ta kafar You tube a internet.

Shugaban Kungiyar Boko Haram a Najeriya Iman Abubakar Shekau a sakonsa ga shugaba Jonathan.
Shugaban Kungiyar Boko Haram a Najeriya Iman Abubakar Shekau a sakonsa ga shugaba Jonathan. REUTERS/IntelCenter/Handout
Talla

Sakon na tsawon mintina 15, ya nuna hoton shugaban mai suna Imam Abu Muhammad Abububakar bin Muhammad shekau sanye da wata rigar garkuwar yaki mai launin tufafin Soji da bindogi a gefensa dama da hagu.

A cewarsa, kiristoci da dukkan al’umma sun san yadda aka murkushe su tare da kai masu hare hare, don haka ne suka fito domin mayar da martani ta hanyar dokokin da Allah Ya shata.

Malam shekau yace, wannan rikicin yafi karfin Jonathan. Domin yasan yadda aka kashe masu mabiya da shugabansu Muhammad Yusuf.

Akwai dai hare hare da dama da kungiyar ta yi ikirarin daukar nauyi.

A watan Ogosta an kai hari a ginin Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a birnin Abuja inda mutane 24 suka mutu. A ranar kirsimeti an kai wasu hare hare a warin ibadar kiristoci da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 37.

03:55

Sanata Abdul Ningi

Sai dai Shugaban kungiyar yace wannan aiki da suke yi aiki ne na Allah tare da kiran al’ummar musulmi su fahimci yakin da suke yi domin basu da wani nufi sai taimakon Addinin Allah.

Wannan sakon na Boko Haram na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar dattijan kasar suka gana game da matsalar tsaro da ke addabar Najeriya. a Hirarsa da Rediyo Faransa, Senata Abdul Ningi yace shugabanni a Najeriya ya dace su dauki mataki ba tare da nuna yatsa ga wani addini ba, illa kokarin daukar mataki saboda matsalar ta shafi bangaren addinin Islama da addinin Kirista a Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.