Isa ga babban shafi
Amurka-Isra'ila

Obama ya tattauna da Netanyahu game da kisan masanin Nukiliyar Iran

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya tattauna da Fira Ministan kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, ta wayar Salula, kwana daya bayan kasar Iran ta zargi kasashen biyu da kitsa kisan masanin Nukiliyarta. Shugabannin biyu sun ce Iran ta dauki kaddarar kisan malaminta bisa gazawar cim ma bukatunsu.

Shugaban kasar Amurka Barack Obama
Shugaban kasar Amurka Barack Obama REUTERS / Kevin Lamarque
Talla

Wasu bayanai daga fadar White House, na cewa Shugabannin biyu sun tattauna zargin da kasar Iran ke yi masu ne, da kuma batun ganin kasar Iran bata aiwatar da bukatun da aka gabatar mata ba akan aikin Nukiliya da take yi.

Bayanan na cewa Shugaba Barack Obama ya nanata burin Amurka na tabbatar da tsaron kasar Isra’ila, tare da neman tuntubar juna.

Sanarwar na cewa shugabnnin sun tabo batun zaman muhawara tsakanin Isra’ila da Falesdinu da kasar Jordan ta shirya a kwanan baya, inda Shugaban kasar Amurka ke cewa burinsu shi ne tabbatar da zaman lafiya, tsakanin kasashen biyu.

A makon gobe ne dai ake saran Shugaba Obama zai gana da Sarki Abdallah na Jordan, inda zai sake tabo batun kasar Isra’ila da Falestinawa.

Har yanzu dai kasar Amurka na ci gaba da karyata zargin hannu wajen kisan masanin kimiyar kasar Iran Mostapha Ahmadi Roshan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.