Isa ga babban shafi
Najeriya

An janye yajin aiki a Najeriya, amma kungiyar kwadago ta rabu biyu

A Najeriya Uwar kungiyar kwadagon kasar ta janye yanje yajin aikin gama-gari da aka kwashe tsawon mako ana gudanarwa bayan shugaban Jonathan ya rage farashin Mai zuwa N97, amma wasu kungiyoyin kwadagon a Jahohi sun yi watsi da matakin uwar kungiyar na kawo karshen zanga-zanga da yajin aikin domin nuna adawa da tsadar Man fetur.

An fara bude kasuwa a Birnin Lagas a Najeriya bayan kwashe tsawon mako daya ana yajin aiki.
An fara bude kasuwa a Birnin Lagas a Najeriya bayan kwashe tsawon mako daya ana yajin aiki. REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Kungiyar kwadagon reshen jahar Kano tace zata ci gaba da yajin aiki da zanga-zanga duk da matakin janye yajin aikin da uwar kungiyar ta kasa ta yi.

A cewar Dan Guguwa shugaban kungiyar a Kano, Uwar kungiyar bata tuntube su ba lokacin da aka dauki matakin janye yajin aikin.

00:32

Kwamred Hashimu Muhammed Gital

Amma shugaban Kungiyar kwadago a Jihar Bauchi, Comrade Hashimu Muhammed Gital yace sun amince da matakin amma uwar kungiyar ta kasa bata tuntube su wajen janye yajin aikin ba.

Tun kafin sanarwar janye yajin aikin ne dai dururuwan mutane a sassan bangarorin jahohin arewa da reshen kudu masu yammaci suka fito kan tituna domin ci gaba da zanga-zanga karkashin jagorancin kungiyar kwadago.

Da safiyar Litinin ne dai shugaba Goodluck Jonathan ya bayar da sanarwar rage farashin man daga Naira 141 zuwa naira 97, amma kungiyoyin fararen hula sun yi watsi da matakin tare da kiran mayar da farashin asali na Naira 65 kowacce lita.

Sai dai shugaba Jonathan Yace ya yanke matakin rage farashin ne bayan ya tuntubi gwamnoni da shugabannin majalisar dokokin kasar.

An kwashe tsawon mako guda ana zanga-zanga a cikin kasar, kuma mutane da dama ne suka rasa rayukansu bisa arangama tsakanin masu zanga-zanga da ‘jami'an tsaro.

Masana tattalin arziki da dama suna ganin janye tallafi ita ce hanyar da zata bude samar da ayyukan ci gaba a kasar domin gwamnati tana hasara ga tallafin, sai dai masu zanga-zanga suna ganin Tallafin ita ce hanyar da suke more arzikin man da Allah ya azurta kasar da shi.

Rehoton Wakilin RFI Kabir Yusuf Daga Abuja

Masu zanga-zangar sun bukaci gwamnati yaki da cin hanci da rashawa da ya yi katutu a cikin kasar tare da datse albashin manyan Jami’an gwamnati da ‘Yan majalisa, kafin daukar matakin janye tallafin.

Amma yanzu haka gwamnatin kasar ta kafa kwamiti wadanda zasu diba ayyukan kudaden da za’a yi amfani da su bayan janye Tallafin. Ministan man Fetur Diezani Alison-Madueke ta bukaci hukumar EFCC da ke yaki da cin hanci a kasar sa ido ga ayyukan kudaden da aka janye na Tallafin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.