Isa ga babban shafi

Isra'ila ta ce za ta kutsa Rafah a Ramadan idan Hamas ba ta saki mutanenta ba

Isra’ila za ta aiwatar da barazanar da ta yi na mummunn hari a Rafah a wata mai zuwa idan har kungiyar Hamas ba ta saki wadanda take garkuwa da su a farkon watan Ramadan ba, kamar yadda daya daga cikin mambobin majalisar aiwatar da yaki ta Isra’ila, Benny Gantz ya bayyana a ranar Lahadi.

 Benny Gantz, mamba a majalisar aiwatar da yaki ta Isra'ila.
Benny Gantz, mamba a majalisar aiwatar da yaki ta Isra'ila. AFP - EMMANUEL DUNAND
Talla

Gantz ya ce dole ne Isra’ila ta shaida wa duniya da kuma shugabannin Hamas cewa idan har ba a saki wadanda ake garkuwa da su a cikin Gaza zuwa lokacin Ramadan ba, za a ci gaba da wannan yaki a ko ina, har da birnin Rafah.

A ranar 10 ga watan Maris ne ake sa ran Musulmai za su fara azumtar watan Ramadan a fadin duniya.

Tun da farko gwamnatin Isra’ila ba ta bada wani wa’adi a game da shirinta na kustawa cikin Rafah ba, birnin da ke dauke da akasarin Falasdinawa miliyan 1 da dubu dari 7 da ke neman mafaka.

Saboda fargabar irin barnar rayuka da za a yi a Rafah, gwamnatocin kasashe da kungiyoyin agaji sun yi ta kira ga Israila ta yi hakuri da batun shiga Rafah, birnin na karshe da dakarun Isra’ilar ba su shiga ba a yayin yakin da aka shafe watanni ana yi.

Duk da matsin lamba da ke karuwa daga kasashen duniya, ciki har da magiya ta kai tsaye daga shugaban Amurka, Joe Biden, Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya zake cewa yakin ba zai kammalu ba idan dakarunsa ba su kutsa cikin Rafah ba.

Isra’ila ta ce ta yi amannar cewa wadanda aka yi garkuwa da su da ma jagororin Hamas su na cikin Rafah a halin da ake ciki.

Mayakan Hamas sun dauki mutane 250 a harin da suka kai Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata, inda suka kashe mutane dubu 1 da dari 1 da 60, lamarin da ya haddasa yakin da ke gudana a halin yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.