Isa ga babban shafi

Sojin Isra'ila fiye da dubu 2 sun samu nakasar dindindin a Gaza

Wasu alkaluma da gidan talabijin din Isra’ila na Channel 12 ya fitar sun nuna yadda zuwa yanzu Sojin kasar fiye da dubu 2 suka samu nakasa ta dindindin sakamakon jikkatar da suka yi a hare-haren da kasar ke ci gaba da kai wa Gaza.

Sojojin Isra'ila da ke ci gaba da yiwa Falasdinawa kisan kare dangi.
Sojojin Isra'ila da ke ci gaba da yiwa Falasdinawa kisan kare dangi. via REUTERS - ISRAEL DEFENSE FORCES
Talla

Alkaluman sun ce adadin na fiye da Soji dubu 2 wani bangare ne na Sojoji akalla dubu 5 da yanzu haka ke karbar kulawa a asibitoci bayan samun munanan raunuka a Gaza.

A cewar alkaluman kashi 58 cikin dari na adadin sojojin da suka samu raunukan babu tabbacin su iya dawowa daidai face sun hadu da nakasa ta har abada.

Wannan alkaluma na zuwa a dai dai lokacin da wasu alkaluman ma'aikatar tsaron kasar ke tabbatar da mutuwar Sojinta fiye da 175 daga watan Oktoba zuwa yanzu. 

Sai dai wasu alkaluma na daban da jaridar Aljazeera ta fitar sun nuna cewa kashi 7 na Sojojin Isra’ilan sun samu matsalar kwakwalwa a yakin da suke a Gaza.

Zuwa yanzu dai Isra’ila ta kashe Falasdinawan da yawansu ya kai dubu 22 da 432 tun bayan faro kisan kare dangin a Gaza ranar 7 ga watan Oktoban bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.