Isa ga babban shafi

Isra'ila ta tsaurara hare-hare kan fararen hular da ke tsakiyar Gaza

Hukumomin lafiyar Falasdinu sun fitar da sanarwar cewa, harin sama da Isra’ila ta kai cikin dare a yankin Gaza da sojojinta suka yiwa kawanya, ya kashe akalla mutane 78, yayin da take ci gaba da gwabza yaki tsakaninta da Hamas.

Yadda wasu iyalai ke laluben 'yan uwansu da baraguzan gine-gine ya danne a yankin Gaza.
Yadda wasu iyalai ke laluben 'yan uwansu da baraguzan gine-gine ya danne a yankin Gaza. © ARAFAT BARBAKH / Reuters
Talla

Harin da aka fara kaddamarwa cikin tsakiyar dare zuwa wayewar garin Litinin, mazauna yankin da kafofin yada labaran Falasdinu, sun ce Isra’ila ta kaddamar da shi ta sama da kuma kasa a yankin Al-Bureij da ke tsakiyar Gaza.

Mai magana da yawun ma’aikatar lafiya ta Falasdinu, Ashraf Al-Qidra, ya ce da dama daga cikin wadanda harin ya shafa mata ne da kananan yara.

Mazauna sansanin ‘yan gudun hijirar da ke tsakiyar Gaza sun ce, sun kwana cikin fargaba saboda yadda jiragen saman Isra’ila suka rika barin wuta cikin dare, da kuma samamen da sojojinta ke yi a gidaje da kan hanya, musamman a Al-Nuseirat da kuma Al-Maghazi.

Da dama daga cikin mazauna yankin Bureij na ta mika kokon bararsu  a kafafen sada zumunta, da a taimaka musu da mafaka.

Hukumomin Isra’ila sun ce suna tattara bayanan yadda aka kai hari yankin Maghazi, yayin da suka ce suna takaita hare-hare kan fararen hula.

Kungiyar agaji ta Falasdinu ta wallafa bidiyon yadda harin na Isra’ila ya lalata hanyoyi, abinda ya haifar da tarnaki ga shirin mika wadanda suka samu raunuka asibiti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.