Isa ga babban shafi

Izra'ila ta kara yawan hare harenta kan Gaza a ya yin da MDD ta bukacin isar da kayan agaji

Sojojin Israela sun kara kaimi hare haren da su ke yi kan Gaza, inda lamuran ayukan jinkai ke ci gaba da tabarbarewa, bayan da a jiya juma'a MDD ta cimma wani dan takaitacen kudiri, karkashin matsin lambara Amuruka, da ya bukaci Izraela ta daga kafa a samu damar da isar kayyakin agajin jinkai ga falestinawan yankunan da ta killace.

wata fashewa a Rafah, dake kudancin Zirin Gaza a ci gaba da da kara kaimin hare haren da izraela ke yi kan falestinawa.
wata fashewa a Rafah, dake kudancin Zirin Gaza a ci gaba da da kara kaimin hare haren da izraela ke yi kan falestinawa. AFP - SAID KHATIB
Talla

Bayan share tsawon kwanaki ana tattaunawa, daga karshe dai a yau juma’a Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kuduri da ke neman Isra’ila ta bayar da damar shigar da kayayyakin jinkai a yankin Gaza. To sai dai wannan kuduri bai bukaci a tsagaita wuta ba saboda rashin amincewar Amurka. 

Wannan kuduri da ya samu goyon bayan kasashe 13, biyu suka yi rowar kuri’unsu wato Amurka da Rasha, ya bukaci bangarorin da ke da hannu a wannan rikici da su bayar da damar ga jami’an agaji domin shiga a yankin na Gaza ba tare da an tursasa ko kuma razana su ba. 

Kazalika kudurin ya nemi a bayar da dama yin amfani da duk wata hanya matukar dai tana shiga a zirin na Gaza domin kai wa milyoyin mutane abinci, ruwan sha, magunguna da sauran abubuwan bukata na yau da kullum. 

Jakadiyar Hadaddiyar Daular Larabawa Lana Zaki Nusseibeh wadda ta gabatar da kudurin gaban MDD, ta ce duk da yake ba abin da suka bukata ne Kwamitin Sulhun ya amince da shi ba, amma wannan kudurin zai taimaka domin samar wa mazauna Gaza sauki sakamakon kuncin da suke fuskanta. 

To sai dai lura da irin kalaman da suke fitowa daga jami’na Isra’ila, manazarta na ganin cewa da wuya wannan daftari ya yi tasirin da ake bukata, lura da cewa babu tabbas idan har za a dakatar da hare-haren ta bama-bamai da ake kai wa Gaza, irin fargabat da Babban Magatakardar MDD Antonio Guterres ya nuna a jawabinsa jim kadan bayan kada kuri’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.