Isa ga babban shafi

Shugabannin kasashen Africa sun yi Allah wadai da hare-haren Isra'ila a Gaza

Shugabannin kasashen Africa sun yi Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ke kaddamarwa kan Gaza da sunan kare kai, yayin da suka bukaci Kasar ta dakatar da barin wutar  ba tare da bata lokaci ba.

Tambarin kungiyar AU
Tambarin kungiyar AU AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Moussa Faki Mahamat, shugaban majalisar gudanarwar kungiyar ya ce wannan luguden wuta, babu abinda ke cikin sa illa cin zali da cin zarafi, kuma lokaci yayi da duniya zata mayar da Isra’ila cikin hayyacin ta.

Kalaman na Faki na zuwa ne bayan doguwar makala da Prime ministan Falasdinu Mohammed Shtayyeh ya karanta a wajen taron.

Shugabannin sun sanar da goyon bayan su ga neman tsagaita wuta da kasashen duniya ke yi.

Wannan yaki na cikin mafiya tashin hankali da duniya ta gani a tarihi, don haka lokaci yayi da ya kamata a dasa masa aya a cewar Moussa Faki Mahamat.

A nasa bangaren Azali Assoumani, shugaban kungiyar AU mai barin gado, ya yabawa Africa ta kudu kan karar Isra’ila da ta shigar gaban kotun duniya, duk da cewa hakan bai yi wani tasiri ba, amma tabbas ya nuna yadda kasashen Africa ke  adawa da wannan aiki.

Duk da cewa Isra’ila ta musanta aikata laifukan yaki da yunkurin kisan kare dangi, amma babu makawa abinda take yi a Gaza bashi da banbanci da abinda ake zargin ta da aikatawa a cewa kungiyar ta AU.

Wannan ya sake tabbatar da matsayar kasashen Africa game da aikin na Isra’ila bayan da suka sallami wakilinta daga taron su na bara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.