Isa ga babban shafi

Hamas ta yi gargadin hare-haren Isra'ila a Rafah su kawo tsaiko a tattaunawarsu

Kungiyar Hamas ta gargadi Isra'ila akan cewa farmakin da ta ke yin a kasa a Rafah, yankin da ke cike da tarin jama'ar Gaza da suka rasa matsugunansu, zai kawo cikas ga shirin sakin fursunoni nan gaba, a yayin da shugaba Joe Biden na Amurka ya bukaci kare fararen hula a yankin da aka yi wa kawanya.

yankin Rafah da Isra'Ila ke kai hare hare ta kasa
yankin Rafah da Isra'Ila ke kai hare hare ta kasa AP - Hatem Ali
Talla

Dangane da yadda Isra’ila ke ci gaba da karin harin a yankin na Rafah mai tarin jama’a gwamnatocin kasashe hada da babbar kawar Isra’ila wato Amurka da sauran kungiyoyi da ke aikin ba da agaji sun nuna damuwar su game da yadda Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ke zurfafa barin wuta a kudancin birnin na Gaza.

Yankin na Rafah dai da ke da iyaka da Masar ya kasance mafaka daya tilo kuma ta karshe ga Falasdinawa da suka fice daga zirin Gaza da Isra’ila ke ruwan bama bamai bayan da ta shafe watanni 4 da mamayar yankin.

A yayin da ake kan gwabza yakin ne firaministan Isra’ila ya umarci dakarunsa da su kara azama wajen cigaba da yin samame a yankin na Rafah.

Sai dai harin da Isra’ila ke kara fadadawa a Rafah ya sanya shugaban Hamas furta cewar hakan na iya haifar da tsaiko ga Shirin da ake yi na shirin sakin wadanda ake kokarin ganin sun shaki iskar ‘yanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.