Isa ga babban shafi

Dubban mutane sun gudanar da zanga zangar neman kawo karshe zubar da jini a Gaza

A yayin da aka shiga kwanaki 100 da soma rikicin Israila da Falasdinu, dubban mutane daga sassan kasashen duniya ne suka fantsama a kan tituna, don neman kawo karshen zubar da jini da Israila ke yi a zirrin Gaza. 

Masu zanga zanga a birnin New York
Masu zanga zanga a birnin New York © Charly Triballeau / AFP
Talla

Tun a jiya asabar ne dandazon mutane suka gudanar da tattake a kasashen Malaysia da Afrika ta kudu da Birtaniya da Indonesia sannan Thailand da Japan da Italiya da Girka da kuma Pakistan.

Akasari masu tattaken sun taru ne a harabar ofishin jakadancin Amurka dake kasashen su, kuma baya ga dora alhakin tsanantar yakin a kan Amurkan sun kuma bukaci ta isarwa Israila sakon su na batun tsagaita wuta. 

Wasu masu zanga zangar neman kawo karshen zubar da jini a Gaza
Wasu masu zanga zangar neman kawo karshen zubar da jini a Gaza REUTERS - HOLLIE ADAMS

Ko a jiya asabar Israilan ta cigaba da barin wuta a zirrin Gaza, inda ta sha alwashin tsananta hare haren da ta ke kai wa domin ganin bayan Mayakan Hamas. 

Firaminjstan Israila Benjamin Netanyahu ya ce kasarsa ba za ta ja da baya ba saboda kararta da aka shigar a babban kotun duniya dake birnin Hague, inda ta musanta zarge zargen da ake mata na take hakkokin biladama, da yin kisan kare dangi a Gaza. 

Netanyahu ya ce babu wanda ya isa ya taka musu birki a hare haren da su ke kaiwa yanzu haka, hatta kotun duniya ICJ, da dakarun Houthi da na Hezbollah masu marawa gwamnatin Iran baya. 

Firaministan israila Benjamin Netanyahu
Firaministan israila Benjamin Netanyahu via REUTERS - POOL

Sama da watanni 3 kenan da soma yakin Israila da Falasdinu, wanda yayi sanadiyar mutuwar akalla Falasdinawa dubu 23,843, wasu sama da dubu 60 kuma suma jikkata, yayin da zirrin Gaza mai alumma kusan miliyan biyu da rabi ya koma kupai. 

Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce harin da Israila ta kai kudancin birnin Rafah, ya yi sanadiyar rushe wani gida mai dauke da wasu iyalai biyu da rikicin ya daidaita, inda akalla mutane 10 daga cikin su suka mutu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.