Isa ga babban shafi

Hana tallafi ga 'yan gudun hijirar Gaza karan tsaye ne ga kotu kan kare dangi-MDD

Wata kwarariya ta Majalisar Dinkin Duniya taa ce dakatar da bai wa Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijrar Falasdinu  da wasu kasashe   suka yi karan tsaye ne ga hukuncin da kotu ta yanke cewa a samar da agaji a ga al’ummar Gaza, kuma yana iya zama watsi da yarjejeniyar kasa da kasa ta  hana kisan kare dangi.

Kwararru sun jaddada mahimmancin ci gaba da tallafa wa hukumar kula da 'yan gudun hijirar Falasdinu a wannan lokaci.
Kwararru sun jaddada mahimmancin ci gaba da tallafa wa hukumar kula da 'yan gudun hijirar Falasdinu a wannan lokaci. AFP/File
Talla

Francesca Albanese, ta bayyana haka ne a yayin da take mayar da martani ga matakin da kasashen suka dauka na dakatar da tallafi ga hukumar, sakamakon zargin da Isra’ila ta yi cewa ma’aikatanta suna da hannu a harin da Hams ta kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba.

 

Dimbim kasashe  da suka hada da  Finland, Jamus  da Italiya ne suka sanar da janye tallafin da suke bai wa hukumar kula dfa ‘yan gudun hijirar Falasdinu.

Majalisar Dinkin Duniya, wadda ta kadu a kan wannan al'amari ta sha alwashin gdanar da bincike a kan wannan zargi da Isra'ila ta  yi wa wasu ma'ikatanta da ke aiki a Zirin Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.