Isa ga babban shafi

Isra'ila ta yi barazanar dakatar da ayyukan hukumar 'yan gudun hijirar Falasdinu a Gaza

Isra’ila ta yi barazanar dakatar da ayyukan Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinu a Gaza baya wannan yaki da ke gudana, biyo bayan zargin da ta yi wa ma’aikatan hukumar da dama da hannu a harin da Hamas ta kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba.

Fira Ministan Isra'ila, Benyamin Netanyahu.
Fira Ministan Isra'ila, Benyamin Netanyahu. AP - Ronen Zvulun
Talla

Ministan harkokin wajen   Isra’ila, Israel Katz ne ya bayyana haka a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X, wanda a da ake kira Twitter, inda ya kara da  cewa Isra’ilar za ta nemi  gudummawar tabbatuwar hakan daga manyan masu bai wa hukumar gudummawa kamar Amurka da Birtaniya.

A Asabar din nan kungiyar Hamas ta yankin Falasdinawa ta caccaki wannan barazanar ta Isra’ila, tana mai bukatar Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyi da kada su fada wa barazanar.

Isra'ila ta fara kai hare -hare Zirin Gaza ne biyo bayan harin da mayakan Hamas suka kai cikin kasarta, inda suka kashe sma da mutane dubu 1 da dari 4, ssuka kuma yi awon gaba da mutane kusan 100, abin da ya fusata mahukuntan kasar, wadanda suka sha alwashin kawar da kungiyar Hamas.

Ya zuwa yanzu hare haren da Isra'ila ke kai wa Zirin Gaza ba kakkautawa ya yi sanadin mutuwar mutane kusan dubu 25, ya kuma daidaita daruruwan dubai, lamarin da ya harzuka da dama a fadin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.