Isa ga babban shafi

Isra'ila ta yi watsi da sharuddan Hamas da ke neman kawo karshen yaki a Gaza

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da sharuddan da Hamas ta gindaya gabanin iya kawo karshen yakin da ke tsakaninsu wanda ya kunshi sakin ilahirin fursunoni da kuma ficewar Sojojin Isra’ila daga Gaza, wanda zai baiwa kungiyar damar ci gaba da jan ragamar yankin.

Firaminstan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Firaminstan Isra'ila Benjamin Netanyahu. © Abir Sultan / AP
Talla

A jawabin Netanyahu, ya bayyana cewa Hamas ta gindaya sharudda masu alaka da kawo karshen yakin da kuma janye ilahirin sojojin Isra’ila daga Gaza kana da sakin Fursunonin Falasdinawan da ke tsare a kasar ta Yahudu, fursunonin da Netanyahu ke bayyana da makasa da wadanda suka aikata fyade.

A cewar Netanyahu ko kadan, ba zai amince da sharuddan ba, haka zalika ba zai dakata da yakin ba, har sai ilahirin mayakan Hamas sun mika wuya gareshi.

Kalaman na Netanyahu na zuwa a dai dai lokacin da babban jami’in diflomasiyyar Turai Joseph Borell ke cewa batun iya kawo karshen Hamas lamari ne da bazai yiwu ba, kuma hanya daya tilo ta kawo karshen yakin shi ne samar da kasar Falasdinu.

Duk da yadda aka shafe shekaru ana tafka muhawara kan batun samar da kasar Falasdinu a zauren Majalisar Dinkin Duniya, har zuwa yanzu Amurka na ci gaba da jan kafa tare da nuna halin ko inkula ba tare da nuna goyon bayan kudirin ba, duk da kasancewarta wadda za ta iya tabbatar da hakan.

Babban jami’in Hamas Sami Abu Zuhri ya bayyana cewa jiragen Sojin Isra’ila sun ci gaba da ruwan bama-bamai kan yankin Khan Younis da ke kudancin zirin gaza bayan da mahukuntan kasar suka yi watsi da sharuddan da Hamas ta gindaya lamarin da acewarsa ke nuna rashin tabbas kan yiwuwar komawar fursunonin kasar gida.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.