Isa ga babban shafi

Kasashe 9 sun dakatar da taimakawa 'yan gudun hijirar yankin Falasdinu

Kasashe da dama daga cikin wadanda ke bai wa Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinu gudmmawa sun bayyana dakatar da duk wata gudummawa, biyo baya zargin da Isra’ila ta yi cewa ma’aikatan hukumar da dama ne ke da hannu a harin da Hamas ta kai mata a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata.

Karin kasashe sun sanar da dakaar da bai wa Hukumar Kula da 'Yanb gudun Hijirar Falasdinu gudummawa.
Karin kasashe sun sanar da dakaar da bai wa Hukumar Kula da 'Yanb gudun Hijirar Falasdinu gudummawa. AFP - MAHMUD HAMS
Talla

Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da martani ba tare da bata lokaci ba, inda ta ce ta sallami ma’aikatanta da dama sakamakon wannan zargi, tana mai shan alwashin cewa za ta gudanar da sahihin bincike a game da lamarin, a yayin da Isra’ila ta sha alwashin dakatar da aikin hukumar a  yankin.

 

Ga abin da kasashen da suka dakatar da bayar da gudummawar ke cewa a game da zargin:

- Australia -

A wannan Asabar, Ministar harkokin wajen Australia, Penny Wong ta ce, ‘a yayin da Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ke gudanar da ayyukan ceto rayuka, Brisbane za ta dakatar da bayar da gudummawa a gare ta na wucin gadi.’ Sai dai duk da haka ta jinjina wa Hukmar sakamakon matakin da ta dauka ba tare da bata lokaci ba.

 

- Canada -

Ministan bunkasa kasashe na Canada, sshi ma a ranar Juma’a ya sanar da matakin kasarsa ta dakatar da bai wa hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya gudummawa na wucin gadi, inda ya  ce ‘Canada za ta gudanar da bincike na kwakwaf a kan wannan zargi’.

- Finland -

Finland, wadda ta kulla yarjejeniyar shekaru 4 da hukumar UNRWA samar mata da Euro miliyan 5 da dubu dari 4, ta sanar da dakatar da yarjejeniyar, inda a wata sanarwa daga ma’aikatar harkokin wajenta, ta ce za ta gudanar da wani ‘bincike mai zaman kansa’.

- Italia -

Ministan harkokin wajen Italia,  Antonio Tajani  y ace kasarsa ta bi sahun kasashen da suka dakatar da samar wa da hukumar UNWRA gudummawa, inda ya kara da  cewa ‘mun kudiri aniyar  samar wa al’ummar Falasdinu taimakon jinkai, tare da kare tsaron Isra’ila’.

- Switzerland -

Switzerland, wadda ta badagudummawar kimanin kudin kasarta ta Swiss farncs miliyan 20, ta fada a ranar Asabar  cewa ba za ta dauki wani mataki na bayar da gudummawarta ta shekarar 2024 ba  har sai an kammala bincike.

- Netherlands -

Miniistan kasuwanci da bunkasa kasa ta na kasar,  Geoffrey van Leeuwen ya sanar da dakatar da bayar da gudummawa ga hukumar  UNRW a yaankin Falasdinu, yana mai bayyana kaduwar kasarsa.

- Birtaniya-

Birtaniya ta bayyana matukar mamaki da wannan zargi da Isra’ila ta yi wa ma’aikatan UNRWA a yankin Falasdinu, kuma ta ta ce ‘za ta dakatar da ba ta gudummawa daga yanzu har sai an kammala bincike’.

- Majalisar Dinkin Duniya -

Shugaban UNRWA, Philippe Lazzarini, ya sha alwashin daukar matakin shari’a a kan duk wani ma’aikacin hukumar da aka samu da hannu a ‘ayyukan taa’addanci’.

Magatakardan Majalisar Dinokin  Duniya, Antonio Guterres ya sha alwashin gudunar da binciken gaggawa, kuma mai zaman kansa a kan wannan lamari, a cewar kakakinsa, Stephane Dujarric.

- Amurka -

Ma’iakatar Tsaron Amurka, a ranar Juma’a ta  sanar da  tata matakin ta dakatar da bai wa UNWRA gudummawa, tana mai cewa ta yi maraba da sanarwar  Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da bincike mai zaman kansa a kan zargin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.